A cikin 'yan shekarun nan, Kamfanin Samsung da sauran masana'antun wayoyin hannu sun fito da wata sabuwar fasaha mai suna virtual RAM, wadda Samsung ke kira da RAM Plus. Wannan tsari yana amfani da wani bangare na ajiyar waya (storage) domin kara karfin RAM na wucin gadi. Mutane da dama suna tunanin cewa hakan zai sa wayarsu ta yi sauri sosai, amma shin gaskiyar lamari ke nan? A cikin wannan makalar, zamu fito da gaskiyar tsarin RAM Plus a wayoyin Samsung domin gane ko yana taimakawa ko kuwa yana kawo tsaiko ne wajen aikin wayar ku.
Domin fahimtar ko RAM Plus yana sauri a wayar Samsung, yana da kyau mu fara gane yadda yake aiki. Waya tana amfani da ainihin RAM wajen sarrafa manhajoji (apps) da ke bude a sa'ilin. Lokacin da RAM ya cika, tsarin RAM Plus zai ware wani bangare na ajiyar wayarka ta ciki (UFS storage) domin adana manhajojin da ba kyai amfani da su sosai a lokacin.
Saurin karanta bayanai na ainihin RAM ya ninka saurin ajiyar ciki na waya sau da dama, wanda ke nufin ajiyar wucin gadi ba za ta taba kai karfin ainihin hardware ba.
A takarda, samun Karin RAM yana da kyau. Amma a gaskiyar lamari, amfani da RAM Plus a wayoyin Samsung masu karfi (flagship) ko matsakaita yana iya rage saurin waya. Domin kuwa idan tsarin Android yana kokarin tura bayanai tsakanin ainihin RAM da ajiyar wucin gadi, wannan musayar tana daukar lokaci da kuma karfin sarrafawa (CPU process).
Idan wayarka tana da ainihin RAM mai yawa (kamar GB 8 ko fiye da haka), a mafi yawan lokuta ba ka bukatar fasahar RAM Plus. Kashe shi yana iya sa wayarka ta rika gudanar da ayyuka cikin santsi da sauri ba tare da tangarda ba. Sai dai idan tsohuwar waya ce mai RAM kalilan (kamar GB 3 ko 4), a nan RAM Plus yana taimakawa wajen hana manhajoji rufe kansu ba tsammani.
Idan kana son gwada saurin wayarka ba tare da wannan tsarin ba, zaka iya shiga Settings > Device Care > Memory, sai ka zabi RAM Plus ka kashe shi (Off) sannan ka sake meyar da wayar (restart).
Shin ka taba gwada kashe RAM Plus a wayarka ta Samsung? Rubuta mana ra'ayoyinka da abin da ka lura da shi a bangaren sharhi!









